Isa ga babban shafi
Duniya - Ramadan

Al'ummar Musulmi sun soma azumin watan Ramadan

Yau Talata al’ummar Musulmi a sassan duniya suka tashi da azumin watan Ramadan, bayan ganin jinjirin wata da yammacin jiya a kasashe da dama ciki har da yankunan Gabas ta Tsakiya da nahiyar Afrika.

Wasu yara a kasar Afghanistan yayin karatun Al-Qur'ani mai girma  a birnin Jalalabad cikin azumin watan Ramadan.
Wasu yara a kasar Afghanistan yayin karatun Al-Qur'ani mai girma a birnin Jalalabad cikin azumin watan Ramadan. AP - Rahmat Gul
Talla

Hukumomin kasar Saudiya ne suka fara sanar da ganin jinjirin watan Ramadan tun a jiya Litinin, abin da ke nufin cewa, yau Talata za a fara azumin Ramadan na shekara ta 1442 bayan hijirar Manzon Allah Salallahu Alaihi Wasallam.

A Najeriya Mai alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar ya tabbatar da rahotannin ganin watan na Ramadan, tare da kuma bayyana Yau Talata a  matsayin daya ga watan.

Musulmi a kasar Pakistan, bayan sayen kayan abincin da za su yi buda baki dasu a cikin azumin watan Ramadan.
Musulmi a kasar Pakistan, bayan sayen kayan abincin da za su yi buda baki dasu a cikin azumin watan Ramadan. AP - Shakil Adil

A bana dai azumin na watan Ramadan ya zo a daidai lokacin da ake fuskantar karuwar adadin masu kamuwa da cutar Korona bayan sake barkewarta zango na 2 a sassan duniya, musamman a nahiyar Turai, inda sabbin alkaluman baya bayan nan suka nuna yawan mutanen da annobar ta kashe ya zarce miliyan 1.

Sai dai a halin da ake ciki za a iya cewa lamarin da sauki a wasu sassan duniya bayan nasarar samar da allurar rigakafi cutar ta Korona da aka soma tsikarawa mutane, abinda ya bada damar sassauta dokokin hana walwalar yaki da annobar a mafi akasarin kasashe, ciki har da batun taro ko cinkoson jama’a.

Musulmi a birnin Khartoum na kasar Sudan yayin shirin rabon abincin buda baki a watan azumin Ramadan.
Musulmi a birnin Khartoum na kasar Sudan yayin shirin rabon abincin buda baki a watan azumin Ramadan. ASSOCIATED PRESS - Abd Raouf

Azumtar watan Ramadan wajibi ne ga Musulman da suka kai shekarun balaga, wadanda kuma suke da lafiya, kasancewarsa daya daga cikin shika-shikan Musulunci guda biyar da suka hada da Imani da Allah da kuma Mazonsa Annabi Muhammad Salllahu Alaihi Wa Sallam, da Sallah da Zakka (ga mai hali) da Hajji (ga mai iko), sai kuma Azumin na watan Ramadan.

Al’ummar Musulmi na kame baki da shawa’a tun daga ketowar alfijir zuwa ga faduwar rana a yayin gudanar da azumin watan Ramadan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.