Isa ga babban shafi
Myanmar

An tuhumi Suu Kyi da karya dokokin sirrin Myanmar

Sojojin Myanmar sun tuhumi  hambararriyar shugabar gwamnatin kasar Aung San Suu Kyi kan karya dokokin sirri na hukumomin kasar da aka kafa tun lokacin mulkin mallaka.

Shugabar Gwamnatin Myanmar Aung San Suu Kyi.
Shugabar Gwamnatin Myanmar Aung San Suu Kyi. Reuters/路透社
Talla

Wannan na zuwa ne a yayin da kasashen duniya ke yin tur da kisan da sojojin ke yi wa fararen hula masu zanga-zanga da juyin mulkin da aka yi wa Suu Kyi.

An kiyasta cewa, mutane 535 suka mutu a zanga-zangar da al’ummar Myanmar suka rika gudanarwa don nuna rashin amicewarsu da hambarar da gwamnatin Suu Kyi.

Ana zargin sojojin da amfani da karfin da ya wuce kima kan masu zanga-zangar da aka fara tun ranar 1 ga watan Fabrairun da ya gabata.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar adawa da tsare Aung San Suu Kyi
Wasu daga cikin masu zanga-zangar adawa da tsare Aung San Suu Kyi . ANONYMOUS/AFP

Tun wancan lokaci, manyan kasashen duniya suka rika sanya takunkuman karayar tattalin arziki kan sojojin da ake zargi da murkushe masu boren.

A baya-bayan nan, Birtaniya wadda ita ce ta yi wa Myanmar mulkin mallaka, ta sanar da sanya takunkumi kan wasu manyan sojoji 11 wadanda ake ganin su ne kanwa-uwar-gami wajen juyin mulkin da kuma hana su tafiye-tafiye.

A bangare guda, Birtaniya ta ware fam miliyan biyar ga Kwamitin Zaman Lafiya na Majalisar Dinkin Duniya don fara aikin tuhumar kasar da mummunan cin zarafin dan adam.

A cewar Birtaniya, tun da aka yi juyin mulkin a ranar 1 ga watan Fabrairun, sojojin suka rufe ido tare da kisan mutane ba-ji-ba-gani da suka hada da kananan yara.

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.