Yan takara biyu ne zasu kara a zaben Ecuador zagaye na biyu
A jiya asabar ne hukumar zaben Ecuador ta fitar da sakamakon zaben shugabancin kasar ,inda ta ayana cewa dan takara Andres Arauz zai kara da tsohon ma’aikacin banki Guillermo Lasso a zagaye na biyu da zai gudana ranar 11 ga watan Afrilu na shekarar bana.
Wallafawa ranar:
Andres Arauz matashi mai shekaru 36 magadin tsohon Shugaban kasar Rafael Correa da ke rayuwa a Belgium tun a shekara ta 2017, ya samu kusan kashi 32 da digo 72 cikin dari na kuri’u,abokin takarrar sa Lasso ya kuma samu kashi 19 da digo 74 cikin dari.
Tawagar yan sa ido a karkashin kungiyar kasashen yankin Amurka OEA ta yaba matuka ganin yada aka tafiyar da wannan zabe,inda akala mutane milyan 13 da dubu dari daya suka kada kuri’u su domin kawo karshen shugabancin Lenin Moreno,wanda jama’ar kasar suka nuna kyama a kan sat un bayan da ya kama karagar mulkin wannan kasa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu