Isa ga babban shafi
Ecuador

Correa ya lashe zaben shugaban kasar Ecuador a karo na uku

Hukumar Zabe a kasar Ecuador, ta sanar da shugaba Rafael Correa a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da akayi jiya, bayan ya samu sama da kashi 50 na kuri’un da aka kada. Yayin da yake jawabi ga magoya bayansa, shugaba Correa da zai yi wa’adi na uku na shekaru hudu, ya ce zai aiwatar da wasu sabbin juyin juya hali dan ganin kasar ta sake samun cigaba. 

Shugaban kasar Ecuador, Rafael Correa, a lokacin da yake bayani ga dumbin magoya bayansa jim kadan bayan lashe zaben shugaban kasa.
Shugaban kasar Ecuador, Rafael Correa, a lokacin da yake bayani ga dumbin magoya bayansa jim kadan bayan lashe zaben shugaban kasa. REUTERS/Gary Granja
Talla

“Babu wanda zai hana wannan juyin juya hali, kuma zamu kafa tarihi.” Dan shakeru Correa dan shekaru 49.

Guillermo Lasso, wanda a day a taba rike mukamin Ministan Kudin kasar shine ya yi takara da Correa ya kuma bayyana amincewarsa da sakamakon zaben jim kadan bayan an fadi sakamakon zaben.

A yanzu haka ana sa ran jam’iyar Correa ce zata lashe mafi aksarin kujeru 137 dake majalisar kasar.

A fagen siyasar duniya kuwa, a shekarar da ta gabata ne, Correa ya tunzura kasashen Amurka da Birtaniya, bayan ya bawa Julian Assange, mutumin dake wallafa bayanan sirri na Wikileaks mafaka a ofishin jakadancin Ecuador dake London, bayan an tuhume shi da laifin yin fyade.

A yanzu haka Correa ya yi kira da a nemi hanyar lumana wajen sasanta rikicin na Assange.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.