Isa ga babban shafi
Faransa

Fasahar 5G na yin illa ga jirgin sama- Masana

Hukumar Kula da Sufurin Jiragen sama ta Faransa  ta bayyana cewar hanyar sadarwar 5G na yi wa sufurin jiragen sama illa, inda ta bukaci fasinjoji da su rika  kashe wayoyin hannunsu a yayin tafiya a cikin jiragen.

Ana yawan cece-kuce kan fasahar 5G
Ana yawan cece-kuce kan fasahar 5G REUTERS/Tingshu Wang
Talla

Mai magana da yawun hukumar ya ce amfani da wayoyin salular da ke dauke da hanyar sadarwar 5G na shafar tafiyar jiragen sama lokacin da jiragen ke sararin samaniya.

Sanarwar ta yi gargadin cewar, tiririn da ke fitowa daga wayoyin na shafar ayyukan jiragen kuma haka na iya haifar da babbar matsala, saboda haka ya dace a kauce wa amfani da wayoyin a lokacin tafiye-tafiye a sararin samaniya.

Har yanzu ana ci gaba da cece-kuce kan illar da fasahar ta 5G ke da ita, inda ko a bara aka rika yayata cewa, fasahar ce ta haifar da annobar coronavirus, amma tuni masana kimiya suka musanta wannan ikirari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.