Isa ga babban shafi
Iran

Iran na ci gaba da karya yarjejeniyar nukiliyarta

Kasashen Faransa da Rasha sun bukaci Iran da ta mutunta yarjejeniyar nukiliyar da ta kulla da manyan kasashen duniya, bayan wani rahotan Hukumar Yaki da Yaduwar makamin nukiliya ya zargi kasar da ci gaba da tace sinadarin uranium.

Wasu daga cikin cibiyoyin nukiliyar kasar Iran
Wasu daga cikin cibiyoyin nukiliyar kasar Iran REUTERS/Raheb Homavandi
Talla

Ministan Harakokin Wajen Faransa a wata sanarwa mai dauke da sanya hannunsa, ya yi fatan Iran za ta ci gaba da mutunta ka’idojin da aka shinfida mata,abinda zai  taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya mai dorewa tsakanin manyan kasashen duniya.

Kazalika Ministan Harakokin Wajen Rasha Ria Novosti ya ce, ya zama wajibi Iran ta yi aiki da ka’idojin da aka gindaya mata.

Ita ma Amurika na sa ran a cimma mafita ta hanyar diflomasiya, yunkurin  da Faransa ta yaba da shi, tsarin nukiliyar na Iran da aka yi wa sunan JCPOA na daga cikin manyan batutuwa da ke ci wa manyan kasashe tuwo a kwarya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.