Coronavirus ta haddasa hasarar dala triliyan 1.3 a fannin yawon bude ido
Wani rahoton hukumar kula da yawon bude ido a duniya ya nuna cewar sashin ya fuskanci koma bayan da ba a taba ganin irinsa ba, saboda tasirin annobar Coronavirus.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Rahoton ya ce sashin yawon bude idanun na duniya ya tafka hasarar kudaden da yawansu ya kai akalla dala triliyan da biliyan 300 a shekarar 2020.
Takaita zirga-zirga ko tafiye tafiye a matsayin matakan yaki da annobar coronavirus, na daga cikin matsalolin da suka janyowa sahin yawon bude idanun koma baya.
Kididdiga dai ta nuna cewa asarar da aka tafka a a shekarar ta 2020, ta rubanya wadda aka gani a 2009, lokacin da tattalin arzikin duniya ya durkushe.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu