Isa ga babban shafi
Coronavirus

Korona ta cigaba da kashe mutane a duniya

Annobar coronavirus ta yi sanadiyar mutuwar mutane 1,876,803 a duniya, tun bayan bulluwarta a watan desembar 2019, kamar yadda sakamakon da Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ya tabbatar.

Wani mai dauke da cutar korona a gadon asibiti a Brazil
Wani mai dauke da cutar korona a gadon asibiti a Brazil REUTERS
Talla

Sama da mutane miliyan 86,868,467 a hukumance gwaji ya tabbatar sun kamu da annobar, daga cikinsu kuma dubu 61,594,450 ke matsayin wadanda suka warke.

Sakamakon dake zuwa a cikin sanarwar da hukumomin kiyon lafiya na kasshen duniya suka bayar bai yi la’akari da lisafin da hukumonin kididigar kasashen Rasha, Spain da Birtaniya suka bayar ba.

Har yanzu Amurka ke kan gaba,inda cutar da kashe mata sama da mutane dubu 365,664 cikin sama da mutane miliyan 21,579,641 da suka harbu.

Sai Brazil dake da sama da mutane dubu 197,777 da suka mutu cikin sama da miliyan 7,812,007 da sukaharbu, sai indiya a matsayi na 3 da yawan mamata 150,151 cikin miliyan 10,375,478 da sukaharbu, sai Mexico ta yi hasarar mutane dubu 128,822 sai kuma Italiya da ta rasa mutane 76,329 cikin sama da miliyan 2,181,619 da suka harbu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.