Isa ga babban shafi
Coronavirus-Kirsimeti

Bukukuwan Kirsimeti na gudana karkashin dokokin takaita walwala

Al'ummar Kirista a sassan duniya ke bikin Kirsimeti dake a matsayin ranar tunawa da haihuwar Yesu Al Masihu.

Bikin ranar Kirsimeti ya zo a daidai lokacin da hukumomi suka takaita walwalar jama'a saboda annobar coronavirus.
Bikin ranar Kirsimeti ya zo a daidai lokacin da hukumomi suka takaita walwalar jama'a saboda annobar coronavirus. Reuters
Talla

Sai dai bikin na bana ya zo ne a karkashin dokokin takaita zirga-zirga, gami da hana cinkoso ko taron jama’a domin dakile yaduwar annobar coronavirus da ta sake barkewa karo na biyu a sassan duniya.

Tuni dai matakan takaita walwalar suka tilasatawa miliyoyin mutane soke shirye-shiryensu na bukukuwan zagayowar ranar ta Kirsimeti, inda a maimakon tarukan da aka saba, a yanzu hukumomi a nahiyoyin duniya suka takaita bukukuwan zuwa cikin gidaje da kananan dakunan taro don kaucewa cinkoso.

A maimakon baiwa gudanar taruka, ko bukukuwan Kirsimeti fifiko a yanzu hankulan hukumomi da jami’an lafiya ya karkata zuwa samun nasarar yiwa mutane allurar rigakafin annobar ta coronavirus.

Kawo yanzu akalla mutane miliyan 1 da dubu 731 da 936 annobar ta halaka a fadin duniya, daga cikin akalla mutane miliyan 78 da dubu 678 da 240 da suka kamu da cutar, sai dai miliyan 49 da dubu 787 da 800 sun warke.

A Amurka kadai rayukan akalla mutane dubu 326 da 232 cutar ta lakume, sai Brazil da ta rasa mutane dubu 189 da 220, sai kuma India kasa ta 3 da annobar tafi yiwa ta’adi, inda ta kashe mutane dubu 146 da 756.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.