Isa ga babban shafi
CPJ

Fiye da 'yan jarida 270 aka daure a bana-CPJ

Kungiyar da ke kare hakkin 'Yan Jarida ta duniya ta CPJ ta bayyana cewar, akalla 'Yan Jarida 274 aka daure a Kasashen duniya a cikin wannan shekara sakamakon yadda gwamnatoci ke tirsasa wa ma’aikatan da ke yada labaran da basa so jama’a su sani.

Dandazon 'yan jarida a bakin aiki
Dandazon 'yan jarida a bakin aiki JOSEPH EID / AFP
Talla

Rahotan da kungiyar ta gabatar ya ce, wannan adadi na daga cikin mafi yawa da aka gani tun bayan lokacin da ta fara tattara alkaluma a farkon shekarar 1990, kuma shi ne karo na 5 da ake samun kusan 'Yan Jarida 250 a cikin shekara guda.

Kungiyar ta bayana kasashen China da Turkiya da Masar da kuma Saudi Arabia a matsayin kasashen da suka fi daure 'Yan Jarida a duniya, yayin da gwamnatoci kan yi amfani da zanga-zanga ko rikicin siyasa wajen kama ma’aikatan yada labaran suna tsarewa.

Rahotan kungiyar ya kuma ce an samu karuwar 'Yan Jarida da kasashen Habasha da Belarus ke tsarewa, musamman lokacin zanga-zangar adawa da shugaba Alexander Lukashenko bayan zaben kasar.

Kungiyar ta ce yayın da babu dan jaridar da aka tsare a Amurka lokacin gabatar da wannan rahoto, 'Yan Sanda a kasar sun kama 'Yan Jarida 110 a cikin wannan shekara mai karewa, kuma an gurfanar da su a kotu saboda dauko rahotannin zanga-zangar cin zarafin da 'Yan sanda ke yi, kuma yanzu haka ana ci gaba da yi wa 12 daga cikinsu shari’a.

Daga karshe kungiyar ta ce an daure 'Yan Jarida 34 a kasashen duniya a bana saboda gabatar da labaran karya, sabanın 31 da aka gani bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.