Isa ga babban shafi
Lebanon

An yanke wa makashin Hariri daurin rai da rai

Kotun kasa da kasa ta yanke hukuncin daurin rai da rai kan wani mamba na kungiyar Hezbollah da ke gudun hijira bayan ta same shi da laifin kashe tsohon Firaministan Lebanon Rafic Hariri da wasu mutane 21 a shekarar 2005.

Kotun da ta yanke hukuncin kisa kan makashin Hariri na Lebanon.
Kotun da ta yanke hukuncin kisa kan makashin Hariri na Lebanon. iroschka VAN DE WOUW / ANP / AFP
Talla

Kotun wadda ke zaune a Netherlands ta yanke wa Salim Ayyash mai shekaru 57 hukuncin ne a bayan idonsa, bisa samun sa da laifin kisa da ta’addanci a harin da kuma ya yi sanadiyar jikkatar mutane 226.

Ayyash na ci gaba da gudun hijira, inda yake samun mafaka karkashin shugaban Kungiyar Shi’a ta Hezbollah, wato Hassan Nasrallah wanda har yanzu ya ki mika shi ga hukumomi.

Kotun wadda ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya ta ce, Mista Ayyash na da hannu a aikin ta’addancin da ya haddasa mutuwar mutane masu yawa.

An samu Ayyash da laifin shiga cikin aikin ta’addancin ta hanyar tayar da abubuwa masu fashewa da suka yi sanadiyar mutumar Hariri da kuma karin mutane 21 baya ga yunkurin kashe wadanda suka samu rauni.

Marigayi Hariri ya rike mukamin Firaministan Lebanon har zuwa lokacin da ya yi murabus a cikin watan Oktoban 2004.

A cikin watan Fabirun 2005 ne, aka kashe Hariri bayan dan kunar-bakin wake ya tarwatsa kansa a cikin wata mota makare da bama-bamai a daidai lokacin da ayarin motocin marigayin ke wucewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.