Isa ga babban shafi
Coronavirus

Corona ta yi raga-raga da harkar sufurin jirage a duniya

Annobar Covid-19 ta matukar haifar da koma-baya ga fannin sufurin jiragen sama na duniya da ba a taba ganin irinsa ba a tarihi.

Kudaden da bangaren sufuri ya samu a bana ba su wuce Dala biliyan 328 ba.
Kudaden da bangaren sufuri ya samu a bana ba su wuce Dala biliyan 328 ba. REUTERS/Regis Duvignau/File Photo
Talla

Shekarar 2020 ta kasance mafi muni ga bangaren sufurin jiragen sama bayan tattalin arzikinsu ya samu gagarumin nakasu.

Kudaden hada-hadar cinikin da sashen sufurin ya samu a wannan shekara ta 2020 ba su wuce Dala biliyan 328, sabanin Dala biliyan 838 da kamfanonin jiragen suka samu a 2019, abin da ke nuna cewa, bangaren sufurin ya samu koma baya da kashi 60 cikin 100.

Yawan fasinjojin da aka yi jigilar su a duniya a bana sun kankance idan aka dauka daga shekara 2003 da fasinjoji biliyan 1.8, wanda hakan ke a matsayin koma-bayan kasa da  kashi 60. 5%, idan aka kwatanta da fasinjojin da kamfanonin jiragen saman suka yi jigilar su a shekara ta 2019, da aka kiyasta cewa sun kai biliyan 4 da rabi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.