Isa ga babban shafi
Amurka

Pennsylvania ta raba gardama tsakanin Trump da Biden

Dan takarar Jam’iyyar Democrat Joe Biden na gab da lashe zaben Amurka bayan ya bai wa shugaba Donald Trump rata mai yawa a kuri’un da aka tattara a Pennsylvania, jihar da ake ganin za ta fayyace makomar ‘yan takaran biyu.

Joe Biden da  Donald Trump
Joe Biden da Donald Trump JIM WATSON, SAUL LOEB / AFP
Talla

Jihar Pennsylvania da wakilanta 20, sun wadatar da Joe Biden mai shekaru 77 zarta adadin da yake bukata na kuri’un wakilan Electoral College 270 kafin ya zama sabon shugaban kasa.

Kodayake har yanzu ba a kammala kidayar dubban kuri’u ba a jihar ta Pennsylvania, musamman a yankunan da Democrat ke da dimbin magoya baya, amma duk da haka Biden ya bai wa Trump rata mai yawa.

A halin yanzu, Biden na da kuri’u 253 na wakilan Electoral College masu tantance wanda zai zama shugaban kasa, yayin da yake sahun gaba a wasu karin jihohi guda uku da suka hada da Arizona da Georgia da Nevada.

Babu tantama alamu sun nuna cewa, Trump na gab da shan kayi a zaben na Amurka, amma shugaban ya nanata cewa, ba zai amince da rashin nasararsa ba, yana mai zargin tafka magudi ba tare da wata hujja ba.

Kwamitin yakin neman zabensa ya fitar da wata sanarwa, inda yake cewa, har yanzu fa, ba a kammala wannan zabe ba.

Rahotanni sun ce, tuni aka tsaurara matakan tsaro ga Biden da iyalansa, sannan an hana jirgin sama keta sararin samaniyar gidansa, yayin da hukumomi suka fara ba shi bayanan da suka shafi tattalin arziki da cutar coronavirus, abin da ke kara tabbatar da cewa, Biden na gab da shiga fadar White House a matsayin sabon shugaban kasar Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.