Isa ga babban shafi
Amurka

Makomar Afrika a zaben Amurka

Masu fashin bakin siyasa sun bayyana cewa, sakamakon zaben shugabancin Amurka na da matukar tasiri kan makomar Afrika wadda ake kallo a matsayin nahiya mai fama da dimbin matsaloli kama daga koma-bayan tattalin arziki da tabarbarewar tsarin kiwon lafiya da rashin kayayyakin more rayuwa da sauransu.

Wani bangare na masu kada kuri'a a Houston na Texas a Amurka.
Wani bangare na masu kada kuri'a a Houston na Texas a Amurka. REUTERS/Go Nakamura
Talla

A yayin zantawarsa da sashen Hausa na RFI, Dr. Abba Sadiq, mai sharhi kan siyasar kasashen duniya ya bayyana cewa, alaka tsakanin Afrika da Amurka za ta inganta muddin Joe Biden ya  lashe zaben kasar.

Dr. Sadiq ya ce, ana kallon shugaban Amurka a matsayin shugaban duniya saboda muhimmancin kasar a doran-kasa, a don haka idan shugaban ya so a samu zaman lafiya a duniya, to za a samu a cewarsa.

Masanin ya bayyana Trump a matsayin shugaban da ya haddasa rikita-rikita a siyasar duniya.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakkiyar hirarsa da Abdoulaye Issa

03:40

Makomar Afrika a zaben Amurka

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.