Isa ga babban shafi
Amurka

Bakaken fata sun yi wa Trump taron dangi

Bisa dukkan alamu bakaken fata sun dukufa domin ganin shugaban Amurka Donald Trump bai koma kan karagar mulki ba wa’adi na biyu, inda suka fito kwansu da kwarkwatarsu a zaben shugabancin kasar tare da jefa kuri’a ga abokin hamayyarsa Joe Biden.

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. AP Photo/Brynn Anderson
Talla

A yayin zantawarsa da sashen Hausa na RFI, Alhaji Bala Musa, wani dan asalin Jamhuriyar Nijar amma mazaunin jihar North Carolina ta Amurka ya bayyana cewa, kabilanci ne babban abin da ya tunzura bakaken yin tururuwa a zaben don ganin bayan Trump.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakkiyar hirarsa da Ahmed Abba.

03:50

Bakaken fata sun yi wa Trump taron dangi

Bakaken na zargin shugaba Trump da nuna musu kyama, suna kokawa kan yadda yake nuna halin ko in kula ga sha’anin da ya shafi bakar fata.

Trump ya sha suka kan kisan da jami’an ‘yan sanda suka yi wa bakar fatar nan George Floyd, lamarin da ya haddasa zanga-zangar Black Lives Matter a sassan Amurka da wasu kasashen duniya.

Alhaji Bala ya ce, akwai Amurkawa fararen fata da ke nuna bacin rai kan yadda Trump ke yin biris da lamurran da suka shafi bakaken fata a Amurka.

Alhaji Bala wanda tuni ya kada kuri’arsa tare da mai dakinsa, ya yi hasashen cewa Joe Biden na Jami’iyyar Democrat ne zai lashe zaben na 2020.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.