Isa ga babban shafi
Amurka-Zabe

Takaitaccen tarihin Joe Biden dan takarar shugabancin Amurka

Joe Biden wanda cikakken sunansa shi ne Joseph Robinette Biden Junior fitaccen dan siyasa kuma tsohon mataimakin shugaban kasa yayin mulkin Barack Obama na cikin jerin mutanen da suka fara rike madafun iko tun suna da karancin shekaru a tarihin Amurka.

Tsohon mataimakin shugaban kasar Amurk  Joe Biden.
Tsohon mataimakin shugaban kasar Amurk Joe Biden. AP Photo/Patrick Semansky
Talla

An haifi Joe Biden ranar 20 ga watan Nuwamban 1942 ya kuma taso a yankunan Scranton da Pennsylvania da New Castle County da kuma Delaware duk a Amurka, gabanin ya kammala digirinsa ta farko a bangaren shari’a cikin shekarar 1968 ya rike mukamin Kansilan New Castle County a 1970 gabanin zama Sanata mai wakiltar New Castle County a 1972 wanda ya bashi damar shiga sahun Sanatoci 60 mafiya karancin shekaru a tarihin Amurka.

Biden wanda ya taso a gida mai Iyalai 6 yana da kanwa mace guda kana ‘yan uwa maza biyu an kuma bayyana sunan mahaifinsa da Josep Robinette Biden Senior da aka haifa 1915 ya mutu a 2002 sai kuma mahaifiyarsa Catherine Jean Biden wadda ta rayu 1917 zuwa 2010, dukkanninsu mabiya darikar Katlika.

Biden ya jima a matsayin mamban kwamitin harkokin wajen majalisar dattijan Amurka gabanin zama shugaban kwamitin dungurugum, inda ya kafa tarihi samar da gagruman sauye-sauye a alakar kasar da ketare.

Dan takarar shugabancin Amurkan karkashin jam’iyyar Democrat wanda ya ki nuna goyon baya ga yakin gabas ta tsakiya cikin 1991 shi ne ya bayar da shawarar shigar da kasashen gabashin Turai cikin kungiyar tsaro ta Nato.

Tun a matakin Firamare Biden ke jagoranci kasancewarsa Monitan ajinsu, inda ya karanta kimiyyar siyasa a matakin farko gabanin samun digiri a bangaren shari’a.

A shekarar 1966 Biden ya auri matarsa ta farko Neilia Hunter inda su ke da yara 3 Joseph Beau Biden na 3 da Robert Hunter Biden tukuna Naomi Christina Biden.

A shekarar 1972 lokacin da Biden ke matsayin Sanata ne ya rasa matarsa Neilia da ‘yarsa Naomi a wani hadarin mota wanda ya sanyashi auren mace ta biyu Jill Biden a shekarar 1977.

Joe Biden wanda kawo yanzu baya shan barasa, yana goyon bayan akidar tsagaita kera makamai da kuma goyon bayan yaki da dumamar yanayi.

Mataimakin shugaban kasar Amurkan na 47 yanzu haka ya na da shekaru 77 a Duniya inda ya ke karawa da Donald Trump a zaben na yau Talata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.