Isa ga babban shafi
Amurka-Zabe

Salon siyasar shugaba Donald Trump na Amurka

Donald John Trump wanda aka Haifa a ranar 14 ga watan Yunin 1946, a gundunmar Queens na birnin New York, shi ne shugaban Amurka na 45 kuma mai ci yanzu haka, gabanin shigarsa harkokin siyasa ya kasance hamshakin ɗan kasuwa kuma mai shiri a gidan talabijin.

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump (AP Photo/Jose Juarez
Talla

A shekarar 1968, Donald John Trump, ya yi digirinsa na farko a fannin nazarin tattalin arziki a Jami’ar Pennsylvania, ya zama shugaban kamfanin kasuwancin harkokin hada-hadar gidaje da gine-gine na mahaifinsa.

Kafin ya sauya masa suna zuwa The Trump Organisation, inda ya fadada ayyukansa zuwa gina sabbin gidaje da sauyawa tsaffi fasali, masamman otel-otel da gidajen caca da kuma filayen wasan kwallon golf.

Mista Trump ya nemi takaran shugabancin Amurka karkashin jam’iyyar Republican a zaben 2016, inda ya yi nasarar bazata kan ‘yar takarar jam’iyyar Democrat Hillary Clinton.

To sai dai zaben na sa da manufofinsa sun haifar da zanga-zanga a sassan Amurka.

A salon mulkinsa shugaba Trump, ya hana matafiya daga kasashe da dama masamman na musulmai zuwa Amurka, yana cewa saboda dalilai ne na tsaro, tare da mika bukatar gina Katanga tsakaninsu da Mexico.

A cikin manufofinsa na kasashen waje kuwa, mista Trump ya bi tsarin bai wa Amurka fifiko, (America First) inda ya janye kasar daga yarjejeniyoyin duniya da dama, ciki har da ta sauyin yanayi ta birnin Paris, da kuma yarjejeniyar nukiliyar Iran.

Ya sanyawa kasar China harajin kan wasu kayayyakinta, abin da ya haifar da zazzafar yakin kasuwanci tsakaninsu, wanda har sai da ya shafi kasashen duniya.

Donald Trump, ya mayar da ofishin jakadancin Amurka da ke Isra'ila zuwa birnin Kudus, sannan ya janye sojojin Amurka daga arewacin Syria, da kuma rage wasu a Afghanistan.

Shugaban ya gana da takwaransa na Korea ta Arewa Kim Jong-un har sau uku, amma tattaunawa game da hana yaduwar makaman nukiliya ta wargaje a cikin shekarar 2019.

Ana ganin Shugaba Trump a matsayin wanda ya yiwa yaki da annobar korona rikon sakainar kashi, inda ya sha watsi da shawarwarin jami’an kiwon lafiya tare da shatata karairayi da dama kan magani ko rigakafin cutar.

Bugu da kari wata tawagar bincike ta musamman karkashin jagorancin Robert Mueller ta gano cewa, Rasha ta yi kutse a zaben 2016 da shugaba Trump ya yi nasara.

Shugaba Donald Trump ya bukaci magoya bayansa da suka kasa su tsare ranar zabe, domin abokin hamayyarsa da jam’iyyar Demokrat na shirya magudi masammam ma da kuri’un da ake kadawa ta kafar intanet.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.