Isa ga babban shafi
Faransa

An fara tuhumar Sarkozy kan karbar kudin Gaddafi

Masu shigar da kara na gwamnatin Faransa na tuhumar tsohon shugaban kasar Nicolas Sarkozy kan zargin sa da amfani da wasu haramtattun kudaden Libya wajen gudanar da yakin neman zabensa a shekarar 2007.

Tsohon shugaban Faransa Nicolas Sarkozy
Tsohon shugaban Faransa Nicolas Sarkozy AFP
Talla

Masu shigar da karar na bincike kan zarge-zargen da ke cewa, tsohon shugaban Libya Mu’ammar Gaddafi ya bai wa Sarkozy Euro miliyan 50 a sirce domin gudanar da yakin neman zabensa a 2007, kuma tun shekarar 2011 aka fara tona asirin wannan alakar.

Daya daga cikin ‘ya’yan marigayi Gaddafi wato Saif al-Islam ya fara fallasa wa duniya wannan al’amari a wancan lokaci.

Yanzu haka an fara tuhumar Sarkozy a hukumance, abin da ke nufin cewa, alkalan kotun Majistiren Faransa sun samu isassun hujjoji game da laifukan da ake zargin sa da aikatawa.

Ko a cikin watan Janairu sai dai jami’an ‘yan sandan Birtaniya suka cafke wani attajiri mai suna Alexandre Djouhri a filin jiragen sama na Heathrow, a wani bangare na gudanar da bincike kan wadannan kudade.

Kodayake Sarkozy ya sha musanta aikata ba daidai ba, inda a kwanakin nan ya bayayana a shafinsa na Facebook cewa, ya kadu da sabbin zarge-zargen da ake yi masa, yana mai alakanta matakin da wani sabon yunkurin yi masa rashin adalci.

Tsohon shugaban na da damar daukaka kara domin kalubalantar tuhumar tasa kamar yadda dokar Faransa ta tanada

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.