Isa ga babban shafi
Amurka

Muna son a yi wa Trump gwajin lafiyarsa- Democrat

Jam'iyyar Democrat a Amurka na bukatar gudanar da bincike kan shugaba Donald Trump domin tabbatar da cewar yana cikin koshin lafiyar da zai iya jagorancin kasar.

Shugaba Donald Trump
Shugaba Donald Trump Tia Dufour/The White House via AP
Talla

Shugabar Majalisar Dokoki Nancy Pelosi ta ce ita da wasu abokan aikinta za su gabatar da kudiri domin amfani da kundin tsarin mulki don bai wa mataimakin shugaban kasa damar karbe iko idan an gano shugaban ba zai iya gudanar da aikinsa ba.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake cacar baki dangane da sake mahawara tsakanin Trump da Joe Biden, inda Biden ke cewa ba zai shiga mahawarar ba sai an tabbatar da lafiyar shugaban, yayin da Trump ke cewa ya warke tsaf, kuma zai ci gaba da yakin neman zabensa a gobe Asabar.

A hirar da ya yi da tashar Fox, Trump ya caccaki Sanata Kamala Harris da ke mara wa Joe Biden baya a takarar shugabansa, inda ya bayyana ta a matsayin wata abin tsoro, yayin da ya ci gaba da bayyana bukatarsa ta ganin an hukunta Biden da tsohon shugaban kasa Barack Obama.

Ganin irin kalaman da shugaba Trump ke yi wadanda basa kan hanya, Pelosi ta bukaci sanya ido sosai kan shugaban saboda yadda baya iya gane abin da ke faruwa kusa da shi, abin da ya harzuka shugaban ya kuma bayyana ta a matsayin mahaukaciyar da tafi dacewa a sanya ido akan ta, inda ya kara da cewa ba a banza ba ake kiran ta mahaukaciya.

Ya zuwa yanzu dai Joe Biden na ci gaba da bai wa Trump tazara a kuri’ar jin ra’ayin jama’a da bangarori da dama ke gudanarwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.