Isa ga babban shafi
Coronavirus

Corona ta lakume rayuka fiye da miliyan 1

HUKUMAR Lafiya ta Duniya ta ce adadin mutanen da cutar korona ta kashe ya kai miliyan guda da dubu 29 da 593, bayan ta kama mutane sama da miliyan 34 cikin su har da shugaban Amurka Donald Trump.

Annobar coronavirus na barazanar saka ta'azzara a sassan duniya.
Annobar coronavirus na barazanar saka ta'azzara a sassan duniya. indiatimes
Talla

Alkaluman da hukumar ta gabatar yau Asabar sun ce, daga cikin mutane miliyan 34 da dubu 683 da 300 da suka harbu da cutar, miliyan 23 da dubu 923 da 600 sun warke, yayin da sauran ke karbar magani a cibiyoyin kula da lafiya.

Hukumar ta ce a jiya Juma’a kawai, mutane dubu 5 da 616 suka mutu a sanadiyar wannan cuta ta coronavirus, yayin da dubu 323 da 984 suka kamu da ita a fadin duniya a jiyan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.