Isa ga babban shafi
Duniya

Sakaci ne ya janyo hatsarin jiragen Boeing da suka halaka kusan mutane 350

Rahoton bincike da kwamitin majalisar dokokin Amurka ya gudanar na nuni da cewa hatsurran da jirage biyu kirar Boeing 737 MAX suka yi tare da haddasa mutuwar rayukan mutane 346, na tabbatar da sakacin kamfanin da ya kera jirgin da kuma hukumar zirga-zirgar jiragen sama ta tarayya.

Jiragen sama  sumfurin Boeing a kasar Amurka
Jiragen sama sumfurin Boeing a kasar Amurka REUTERS/Lindsey Wasson
Talla

An fitar da rahoton ne bayan share watanni 18 kwararri na bincike dangane da musababbin faruwar wadannan hadurra, wato na jirgin Lion Air na Indonesia da kuma Ethiopian Airlines.

Shugaban Kamfanin kera jiragen Boeing, bangaren dake kula da MAX 737 da aka dakatar da aiki da shi a Duniya saboda haduran da aka samu, Eric Lindblad ya bayyana aniyar sa na aje aikin sa, a daidai lokacin da kamfanin ke cigaba da fuskantar matsaloli.

A shekara ta 2019 ne Shugaban kamfanin Kevin McAllister ya bayyana shirin barin aikin Lindblad, a wannan lokaci da kamfanin ke kokarin shawo kan masu tabbatar da ingancin jiragen sama sun amince da sauye sauyen da kamfanin yayi kan samfurin jirgin da ya hallaka mutane 346 a hadura guda biyu.

McAllister ya bayyana cewar wannan mawuyacin lokacin ne a gare su, a daidai lokacin da suka mayar da hankali wajen dawo da ingancin jiragen kamfanin samfurin MAX 737.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.