Isa ga babban shafi
India

India ta kafa tarihi mafi muni kan yawan masu kamuwa da cutar coronavirus

India ta kafa tarihi mafi muni a duniya na fuskantar karuwar masu kamuwa da cutar coronavirus, bayanda ma’aikatar lafiyar kasar ta bayyana gano karin mutane dubu 78 da 761 da suka kamu da cutar a rana guda.

Wani ma'aikacin lafiya a India, yayin yiwa jama'a gwajin cutar coronavirus a jihar Gauhati. 29/8/2020.
Wani ma'aikacin lafiya a India, yayin yiwa jama'a gwajin cutar coronavirus a jihar Gauhati. 29/8/2020. © Anupam Nath/AP Photo
Talla

Karin mutanen ya sanya India karya tarihin da Amurka ta kafa a baya na samun sabbin mutane dubu 77 da 638 da suka kamu da cutar coronavirus a kwana guda, ranar 17 ga watan Yulin da ya gabata.

Yanzu haka dai India mai yawan mutane biliyan 1 da miliyan 300 ce kasa ta uku a duniya bayan Amurka da Brazil da annobar ta coronavirus ta fi yiwa barna, inda a yanzu yawan mutanen da suka kamu da cutar ya zarta miliyan 3 da rabi.

Yanzu haka dai, sabbin alkaluman hukumomin lafiya sun nuna cewa, yawan mutanen da suka kamu da cutar coronavirus mai kassara hanyoyin numfashin dan adam, ya kai miliyan 25 da dubu 29 da 250 a sassan duniya, daga cikinsu kuma dubu 842 da 915 sun rasa rayukansu.

Sai dai kawo yanzu akalla mutane miliyan 16 ne suka warke daga cutar a tsakanin kasashe kusan 200.

Alkaluman hukumomin lafiyar sun kuma nuna cewar kusan kashi 40 cikin 100 na jumillar mutanen miliyan 25 da suka kamu da cutar ta coronavirus na tsakanin Amurka da Brazil, kasashe biyu da annobar ta fi yiwa barna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.