Isa ga babban shafi
Ilimi

COVID-19: Dalibai miliyan 463 basa iya daukar karatu daga gida

Majalisar dinkin duniya tace akalla yara miliyan 463 ne a sassan duniya ba sa iya daukar karatu daga gida, ta hanyar amfani da Internet, da kuma kafofin talabijin da rediyo.

Majalisar Dinkin Duniya tace yara dalibai akalla biliyan 1 da miliyan 500 ne basa iya daukar karatu daga gida ta kafar Internet.
Majalisar Dinkin Duniya tace yara dalibai akalla biliyan 1 da miliyan 500 ne basa iya daukar karatu daga gida ta kafar Internet. Cecil Bo Dzwowa/Shutterstock pic via AFP-Relaxnews
Talla

Bayanin na kunshe ne cikin sabon rahoton majalisar ta wallafa na bincikenta kan cigaban tasirin annobar coronavirus da ta hana miliyoyin yara karatu, bayan tilasta rufe makarantu.

Majalisar dinkin duniyar ta ce yanzu haka dalibai yara akalla biliyan 1 da miliyan 500 ne basa zuwa makaranta saboda annobar coronavirus da tilastawa hukumomin kasashe rufe dubban makarantun domin dakile yaduwar cutar, tasirin da majalisar tace yafi muni a Afrika da sassan Asiya, fiye da a nahiyar Turai.

Rahoton binciken majalisar dinkin duniyar da ya gudana a tsakanin kasashe 100, ya kara da cewar hatta dalibai yaran da suke da damar daukar karatu daga gida ta hanyar Internet, talabijin ko rediyo, za su iya fuskantar matsalolin da suka hada da rashin wurin daukar karatun cikin nutsuwa a gidajensu, yawaitar ayyukan gidan, da kuma lalacewar komfutocin da daliban ke amfani da su a inda babu masu gyara a kusa.

Daga cikin jumillar dalibai yaran da basa iya daukar karatu daga gida ta Internet, kafafen talabijin da rediyo, a sassan duniya, miliyan 67 na gabashi da kudancin Afrika, miliyan 54 a yammaci da tsakiyar Afrika, sai miliyan 80 a yankin Pacific da gabashin nahiyar Asiya.

Sauran daliban da lamarin ya shafa sun hada da miliyan 37 a Yankin Gabas ta Tsakiya da arewacin Afrika, miliyan 147 a kudancin Asiya, sai kuma dalibai miliyan 13 a nahiyar Latin da Caribbean.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.