Isa ga babban shafi
Iran

Mai yiwuwa Iraniyawa miliyan 25 sun kamu da cutar coronavirus - Rouhani

Shugaban Iran Hassan Rouhani ya kiyasta cewar mai yiwuwa yawan 'yan kasar da suka kamu cutar coronavirus ya kai miliyan 25, abinda ya sanya shugaban rokon da a dauke annobar da muhimmanci.

Shugaban Iran Hassan Rouhani.
Shugaban Iran Hassan Rouhani. Iranian Presidency / AFP
Talla

Rouhani yace ma’aikatar lafiyar kasar ta Iran ce ta tattara alkalumman, bayan binciken da ta gudanar.

Shugaban ya kara da cewar, a wani kyasin na daban, kimanin karin Iraniyawa miliyan 30 zuwa 35 ne cikin hadarin kamuwa da cutar ta coronavirus, kusan kashi 50 na yawan al’ummar kasar ta Iran mai yawan mutane miliyan 81 jumilla.

A halin da ake ciki annobar at coronavirus ta fi yiwa Iran illa a yankin gabas ta tsakiya, bayan halaka mata mutane dubu 13 da 979, daga cikin sama da dubu 270 da suka kamu da cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.