Isa ga babban shafi
Duniya

An raba mutane miliyan 80 da gidajensu-MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, akalla mutane kusan miliyan 80 aka tilasta wa tserewa daga muhallinsu sakamakon tashin hankali ko kuma azabtarwa, abin da ke nuna karuwar adadin a cikin shekaru 10.

'Yan gudun hijirar Rohighya
'Yan gudun hijirar Rohighya STR/AFP
Talla

Shugaban Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Filippo Grandi ya ce wannan adadi wanda shi ne kashi guda na al’ummar duniya ba za su iya komawa muhallinsu ba saboda yaki ko azabtarwa ko cin zarafi da makamantan haka.

Jami’in ya ce, a karshen shekarar 2019 kowanne mutuum guda daga cikin mutane 97 da ke duniya an tilasta masa barin muhallinsa bada san ransa ba, abin da ke nuna karuwar matsalar a kasashe irinsu Syria da Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo.

Grandi ya ce ya zuwa karshen shekarar da ta gabata, hukumarsa ta gano cewar mutane miliyan 79 da rabi na rayuwa ne a sansanin ‘yan gudun hijira ko kuma suna neman mafaka a wasu kasashe ko kuma a wuraren da aka kebewa wadanda suka rasa matsugunansu da ke cikin kasashensu, abin da ya nuna karuwar mutane miliyan 9 daga adadin shekarar 2018.

Shugaban hukumar ya ce, tun daga shekarar 2012 kowacce shekara sai an samu adadin da ya zarce na shekarar da ta gabata sakamakon tabarbarewar zamantakewa da kuma tashe-tashen hankula wadanda ke raba jama’a da muhallinsu.

Grandi ya ce, kashi 68 na mutanen da suka rasa matsugunansu sun fito ne daga kasashen Syria da Venezuela da Afghanistan da Sudan ta Kudu da kuma Myanmar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.