Isa ga babban shafi

Kotun Kolin Amurka ta yi watsi da shirin Trump kan baki

Kotun Kolin Amurka tayi watsi da shirin shugaba Donald Trump na hana bakin dake zuwa kasar da yayan su domin samun rayuwa mai inganci a karkashin shirin da ake kira DACA, hukuncin da zai kare irin wadannan mutane 700,000 da yanzu haka ke cikin Amurka.

Masu gangamin shankayin shugaban Amurka Donald Trump a kotun kolin kasar dangane da shirinsa na raba baki na 'ya'yansu
Masu gangamin shankayin shugaban Amurka Donald Trump a kotun kolin kasar dangane da shirinsa na raba baki na 'ya'yansu REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

Alkalan kotun kolin sun ce matakin da shugaba Donald Trump ya dauka na soke shirin da tsohon shugaban kasa Barack Obama ya samar ya zama kama karya a karkashin tsarin tafiyar da ayyukan mulki.

Alkalan kotun 5 suka amince da bukatar soke matsayin shugaba Trump, yayin da 4 suka ki, inda suka bayyana cewar gwamnatin Trump tayi karan tsaye wajen sabawa harkar gudanar da mulki kan batun wajen yunkurin dakatar da shirin.

Wannan dai ba karamar koma baya bane da shugaba Trump wanda ke cigaba da fuskantar matsaloli a daidai lokacin da yake kokarin sake takara domin neman wa’adi na biyu, kuam nan take ya cacaki matsayin kotun.

Bayan hukuncin tsohon shugaba Barack Obama ya bayyana farin cikin sa inda yake cewa nasara ce ga yara baki da iyayen su da suka shiga kasar daga ko ina domin samun rayuwa mai inganci.

Ita ma shugabar Majalisar Dokoki Nancy Pelosi tace hukuncin ya tsawaita shirin da ita da Amurkawa sama da kasha 3 bisa 4 ke goyan bayan sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.