Isa ga babban shafi
Hamada

Duniya na bikin ranar yaki da gurgusowar Hamada

Yau ce ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin yaki da gurgusowar hamada da kuma fari wanda ke matukar illa ga rayuwar Bil adama. Bikin na bana na zuwa ne a daidai lokacin da duniyar ke fuskantar dimbin matsaloli da sauyin yanayin dake shafar ayyukan samar da abinci.

Masana yanayi dai na ci gaba da gargadi kan illolin da ke tattare da sare bishiyo ba tare da maye gurbinsu da wasu ba.
Masana yanayi dai na ci gaba da gargadi kan illolin da ke tattare da sare bishiyo ba tare da maye gurbinsu da wasu ba. Getty Images/Peter Arnold/Martin Harvey
Talla

Bikin na bana zai mayar da hankali kan sauya halayyar jama’a wajen mayar da hankali ganin yadda gurgusowar hamada da gurbacewar kasar noma ke shafar hanyar samar da abinci.

Rahotan Majalisar Dinkin Duniya ya ce yayin da yawan jama’a ke karuwa a duniya, ana samun karuwar bukatar filayen gine ginen gidaje da masana’antu wajen samar da abinci da kiwon dabbobi da kuma samar da tufafi, yayin da filayen ke cigaba da rasa ingancin su.

Majalisar ta ce za’a samu ingantattun filayen noman da za su biya bukatun mutane biliyan 10 da ke duniya a shekarar 2050 idan jama’a sun sauya rayuwar su wajen kare muhalli.

Rahotan ya ce sama da eka biliyan biyu na filayen noma sun lalace, sama da kashi 70 na koramu sun bata, kuma adadin na iya kaiwa kashi 90 nan da shekarar 2050.

Majalisar tace nan da shekarar 2030 aikin samar da abinci a duniya zai bukaci karin eka miliyan 300 na filaye, wadanda yanzu haka hamada ke cigaba da mamaye su.

Rahotan ya bukaci gwamnatoci da su tashi tsaye wajen daukar kwararan matakan kare muhalli da inganat filayen noma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.