Isa ga babban shafi
Falasdinu

Falasdinawa sun gabatar da sabon shirin sasanta rikicin gabas ta tsakiya

Falasdinawa sun gabatar da wani sabon shirin sasanta rikicin Gabas ta tsakiya ga kungiyoyin da ke jagorancin sasanta rikicin da suka hada da Majalisar Dinkin Duniya da Amurka da Rasha da kuma kungiyar kasashen Turai.

Firaministan Falasdinu Mohammad Shtayyeh.
Firaministan Falasdinu Mohammad Shtayyeh. REUTERS/Tiksa Negeri
Talla

Firaministan Falasdinawan Mohammed Shtayyeh ya sanar da gabatar da shirin wanda ya yi karo da wanda shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar wanda ya mallakawa Israila Birnin Kudus da kuma wasu yankunan Falasdinawan.

Shirin da Falasdinawan suka gabatar ya kunshi kirkiro kasar Falasdinu da sake fasalin iyakokin kasar da kuma kawar da kawanyan sojin da Israila ta yi wa yankin.

Kudirin ya kunshi musayar wasu yankuna tsakanin bangarorin biyu a tattaunawar da za’ayi nan gaba kamar yadda Firaministan ya bayyana.

A shirin sa da ya gabatar a watan Janairu, shugaban Amurka Donald Trump ya mikawa Israila tsanukan Jordan da kuma Gabar Yamma da Kogin Jordan wanda ke dauke da Yahudawan Israila sama da 450,000 duk da haramcin dokokin duniya suka yi akai.

Kungiyar kasashen Turai da Majalisar Dinkin Duniya da wasu kasashen Larabawa sun yi watsi da shirin Trump, yayin da kungiyar EU ta ce tana nazari kan matakan da za ta dauka kan Israila wadda yanzu haka ke shirin mamaye karin filayen Falasdinawan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.