Isa ga babban shafi
Brazil

Za mu janye daga Hukumar Lafiya ta Duniya- Brazil

Shugaban Brazil Jair Bolsonaro ya yi barazanar janye kasar daga Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya saboda zargin ta da nuna-son-kai, bayan ta gargadi kasashen duniya dangane da barazanar da ke tattare da shirinsu na janye dokar kulle jama’a a gidajensu don hana bazuwar coronavirus.

Shugaban Brazil Jair Bolsonaro
Shugaban Brazil Jair Bolsonaro REUTERS/Adriano Machado
Talla

A yayin zanta wa da manema labarai a harabar fadar gwamnatinsa, Bolsonaro ya ce, Amurka ta fice daga Hukumar Lafiyar ta WHO, a don haka, shi ma yana nazarin janyewa daga hukumar nan gaba.

A watan jiya ne dai, shugaba Donald Trump mai irin ra’ayin Bolsonaro, ya ce, Amurka za ta kawo kashen alakarta da WHO, yana mai zargin hukumar da zama ‘yar lelen China.

A kalla mutane dubu 396 ne suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar coronavirus a sassan duniya tun bayan barkewarta a karshen shekarar bara a China.

Har yanzu dai Amurka ce ke kan gaba da wannan annoba ta fi yi wa barna, inda ta rasa mutane sama da dubu 109, sai Birtaniya mai mutane fiye da dubu 40, yayin da Brazil da ke matsayi na uku ta yi asarar mutane dubu 29 da doriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.