Isa ga babban shafi
Duniya

Masu bada agaji sun tara dala biliyan 8 don gano maganin corona

Shugabannin kasashen duniya da masu bada agaji da fitattun mutane yau sun tara sama da Dala biliyan 8 domin gudanar da binciken kimiya na gaggawa dan gano maganin cutar coronavirus dake cigaba da lakume rayukan jama’a.

Kwararru kan lafiya da kimiyya a yanzu haka na gudanar da gwaje-gwaje sama da kashi 100 domin gano rigakafi da kuma maganin cutar coronavirus.
Kwararru kan lafiya da kimiyya a yanzu haka na gudanar da gwaje-gwaje sama da kashi 100 domin gano rigakafi da kuma maganin cutar coronavirus. AFP/File/DOUGLAS MAGNO
Talla

Shugabar kungiyar Turai Ursula von der Leyen da ta jagoranci bikin tare da shugaban hukumar lafiya ta duniya Tedros Adhanom Gebreyesus, tace maganin rigakafi ne kawai zai bada damar shawo kan wannan annoba da ta kashe mutane sama da 245,000 kuma sama da 140,000 sun fito ne daga nahiyar Turai.

Manyan kasashen Turai da kasashen Japan da Canada suka bada gudumawa mai tsoka a taron da Amurka taki halarta saboda zargin da take yiwa hukumar lafiya na rufa rufa dangane da annobar.

Sakatare Janar na Majalisar dinkin Duniya da shugaban hukuamr Lafiya Tedros Adhanmom Gebreyesus da shugaban Faransa Emmanuel Macron na daag cikin shugabannin kasashen duniya da suka yi jawabi a taron da aka yi ta bidiyo, yayin kasashen duniya 40 tare da Gidauniyar Bill da Melinda Gates suka bada gudumawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.