Isa ga babban shafi
Afghanistan

Afghanistan na tuhumar Iran da nutsar da 'yan ci rani a ruwa

Gwamnatin Afghanistan ta kaddamar da bincike kan zargin dakarun Iran da tirsasawa Yan ci ranin Afghanistan nitsewa cikin ruwa, lokacin da suka nemi komawa kasar bayan sun gudu zuwa kasar su lokacin da Iran tayi fama da annobar coronavirus.

Kogin Harīrūd da yayi iyaka da Afghanistan da kuma Iran.
Kogin Harīrūd da yayi iyaka da Afghanistan da kuma Iran. Bruno Pagnanelli/Shutterstock.com
Talla

Rahotanni sun ce a ranar juma’a abin tashin hankalin ya auku, lokacin da bakin ‘yan kasar Afghanistan suka nemi shiga Iran ta Yammacin Herat.

Hukumar kare hakkin Bil Adama a Afghanistan tace tayi Magana da wasu da suka tsira daga cikin ‘yan ci ranin kuma sun tabbatar mata da aukuwar lamarin, inda suka ce dakarun Iran sun yi ta duka da azabtar da su, kafin tura su cikin kogin Harirud.

Jami'ai a lardin Herat dake Afghanistan sun sanar da tsamo gawarwakin mutne 12 daga cikin 'yan gudun hijirar daga cikin kogin na Harirud, yayinda mutane 8 suka bace.

Kogin Harirud da yayi iyaka da kasashen na Afghanistan da Iran, na da tsawon kilomita akalla dubu 1 da 100.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.