Isa ga babban shafi
Duniya

Coronavirus ta lakume rayuka sama da dubu 240 a duniya

Adadin Mutanen da suka mutu sakamakon kamuwa da cutar coronavirus a duniya ya zarce 240,000, yayin da kashi 85 na mutanen suka fito daga nahiyar Turai da kuma Amurka.

Ma'aikatan lafiya a Brooklyn dake Amurka, yayin daukar gawar wani mutum da annobar coronavirus ta halaka.
Ma'aikatan lafiya a Brooklyn dake Amurka, yayin daukar gawar wani mutum da annobar coronavirus ta halaka. Angela Weiss/AFP
Talla

Alkaluman da hukumar lafiya ta duniya ta gabatar sun nuna cewar ya zuwa kusan karfe 9 na daren ranar asabar 2 ga watan Mayu, mutanen da suka mutu sun kai 241,682 daga cikin miliyan 3 da dubu 398,390 da suka kamu da cutar.

A nahiyar Turai kawai sama da mutane dubu 141,475 suka mutu daga cikin sama da miliyan guda da dubu 516,635 da suka harbu da cutar.

Annobar coronavirus tafi yiwa Amurka barna bayan halaka mata mutane dubu mutane dubu 65 da 645, sai kuma Italiya mai mutane dubu 28 da 710, sannan Birtaniya mai mutane dubu 28,131, kana Spain mai mutane 25,100 da kuma Faransa mai mutane 24,760.

A nahiyar Afrika jimillar mutane dubu 1 da 730 annobar coronavirus ta halaka, daga cikin mutane dubu 42 da 229 da suka kamu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.