Isa ga babban shafi
Duniya

"Aikin Jarida ba tare da tsoro ko alfarma ba"

Yau take ranar ‘Yan Jaridu ta Duniya, wadda majalisar dinkin duniya ta ware dukkanin ranakun 3 ga watan Mayu na kowace shekara, domin tunawa da karramma ‘Yan Jaridun da suka rasa rayukansu bisa gaskiya a bakin aiki, da kuma wadanda suka fuskanci cin zarafi ko tauye hakki.

Wata 'Yar Jarida a Manila yayin zanga-zanga a harabar fadar shugaban kasar Philippines.  17/1/2018.
Wata 'Yar Jarida a Manila yayin zanga-zanga a harabar fadar shugaban kasar Philippines. 17/1/2018. Reuters
Talla

Taken bikin ranar ‘Yan Jaridun ta duniya na wannan shekara ta 2020, shi ne “Aikin Jarida ba tare da tsoro ko alfarma ba”.

A watan Disambar shekarar 1993 aka taron kasashen da majalisar dinkin duniya ta jagoranta ya cimma matsayar ware ranar 3 ga kowane watan Mayu don bikin ranar ‘Yan Jaridu ta duniya.

A sakonsa da ya aike, sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres, ya ja hankali ne kan cewar, a daidai lokacin da duniya ke fuskantar kaifi da kuma yaduwar annobar coronavirus ko COVID-19, a gefe guda duniyar na fuskantar wata karin annobar daga mugayen mutane ta yada labarai da sauran bayanai na karya kan annobar murar coronavirus.

Sai dai Guterres ya yabawa ‘Yan Jarida da cewar, suna bada muhimmiyar gudunmawa wajen maganin cutar yada labaran bogin gami da munanan bayanai, ta hanyar bayar da sahihan rahotannin bincike, labarai, da kuma fashin bakin kwararru kan annobar coronavirus da a yanzu haka ta addabi duniya.

A Najeriya, shi ma shugaban kasar Muhammadu Buhari jinjinawa ‘Yan Jaridun kasar yayi, kan rawar da suke takawa wajen fadakar da jama’a dangane da annobar coronavirus wadda ke cigaba da lakume rayukan dubban mutane a fadain duniya.

A sanarwar da mai Magana da yawunsa Femi Adeshina ya rabawa manema labarai dangane da bikin ranar ‘yancin Yan Jaridu ta Duniya, shugaba Buhari ya bayyana muhimmancin aikin jaridar wajen sanar da jama’a da kuma fadakar da su musamman a wannan lokaci da cutar COVID-19 ke afkawa jama’a ba tare da kaukautawa ba.

A karshe shugaban ya tabo yadda labaran karya da labaran nuna kyamar ke yiwa aikin jarida illa inda ya bukaci daukar matakan shawo kan su saboda illar da suke yiwa jama’a

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.