Mutane miliyan 50 sun rasa gidajensu dalilin tashe-tashen hankula da bala'o'i
Wani Bincike ya nuna cewar tashin hankali tare da nau’o’in bala’in da aka fuskanta a duniya sun yi sanadiyar raba mutane sama da miliyan 33 da muhallansu a shekarar 2019 da ta gabata, abinda ya jefa su cikin hadarin kamuwa da cutar coronavirus.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Rahoton da kungiyar dake sa ido kan mutanen da suka bar matsugunan su da kuma kungiyar kula da ‘yan gudun hijira ta kasar Norway suka wallafa, ya bayyana cewar sabbin alkalumman da aka samu ya kawo jimillar adadin mutanen da suka rasa matsugunan su zuwa miliyan 50 da dubu 800.
Daraktan kungiyar Alexandra Bilak, tace yanzu haka akwai irin wadannan mutane miliyan 26 da suka tsallaka iyaka suka bar kasashensu domin samun mafaka, kuma a shekarar da ta gabata, an samu irin wadannan mutane miliyan 8 da rabi a kasashe irin su Syria da Jamhuriyar dimokiradiyar congo da Habasha da kuma Sudan ta kudu.
Rahotan yace yanzu haka mutane sama da miliyan 45 suka tsere daga matsugunan su a duniya, cikin su harda kusan miliyan 6 da rabi da suka gudu daga Syria da aka kwashe shekaru 9 ana yaki, yayin da wasu sama da miliyan 5 suka bar gidajen su saboda wasu bala’oi a bara, daga cikin miliyan 25 da suka bar gidajen su bara.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu