Isa ga babban shafi

Ko kun san halin da ake ciki dangane da coronavirus a duniya ?

Yawan mamata sakamakon kamuwa da kwayar cutar Coronavirus na ta karuwa a kasashen duniya inda ya zuwa Alhamis din nan alkaluman mamata suka zarce 21,200 a kasashen duniya 182.

Ma'aikatar Lafiya a Barcelona na kasar Spain
Ma'aikatar Lafiya a Barcelona na kasar Spain REUTERS/Nacho Doce
Talla

Alkaluman mamatan na nuna a kasar Spain jimillar mamata sun kai dubu 4, 089 ya zuwa Alhamis din nan kenan, kasancewar an sami karin mamata 650 cikin sa'o'i 24 da suka gabata, yayinda sabbin mutane dubu 56, 188 suka kamu da cutar.

A kasar Amurka kuwa ya zuwa wayewar garin Alhamis gawaki 1,050 aka samu, yayinda mutane sama da dubu 69 aka samu sabbin kamuwa da wannan cuta.

Wannan yasa ala tilas majalisar Dattawan Amurka zartas da tallafin kudade da suka kai dalar Amurka Trillion 2 duk dai don a yaki cutar.

Sauran kasashen da suka kamu da cutar sun hada da Italia inda aka sami mamata 7,503 yayinda wasu mutanen dubu 74,386 suka kamu.

A kasar China inda cutar ta taso an sami mamata dubu 3,281 daga cikin wadanda suka kamu dubu 81,218.

A kasar Faransa mamata 1,331 aka samu sai kasar Iran mai mamata 2234.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.