Isa ga babban shafi
Turkiya

Erdogan na ganawa da EU kan 'yan gudun hijira

A yau Litinin shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan ke ganawa da mahukuntan Kungiyar Tarayyar Turai a birnin Brussels, a daidai lokacin da ya bukaci Girka da ta bude kan iyakarta domin bai wa ‘yan gudun hijirar Syria damar kwarara cikin Turai .

shugaban Turkiya, Recep Erdogan
shugaban Turkiya, Recep Erdogan Turkish Presidential Press Office/Handout via REUTERS
Talla

A yayin gabatar da jawabi a jiya Lahadi a birnin Santanbul , shugaba Erdogan ya bayyana cewa, zai gana da hukumomin Kungiyar Tarayyar Turai a wannnan Litinin a Belgium.

A cewar shugaban zai tattaunawa da mahukuntan na Turai kan batun shige da fice bayan Turkiya ta bude kan iyakarta, yana mai fatan cewa, zai dawo daga Belgium da mabanbantan sakamako.

Matakin da Turkiya ta dauka na bude kan iyakarta, ya dada rura tankiyar da ke tsakaninta da Kungiyar Tarayyar Turai, baya ga musayar zafafan kalamai tsakaninta da Girka.

Shugaba Erdogan zai gana shugaban Majalisar Tarayyar Turai, Charles Michel da kuma shugaban Hukumar Turai, Ursula von der Leyen a Brussels da misalin karfe 5 na yamma agogon GMT.

Mai magana da yawun shugaban Majalisar EU, ya ce , shugabannin za su tattauna kan abubuwa da dama da suka shafi Kungiyar da Turkiya da suka hada da batun shige da fice da matsalar tsaro da samar da zaman lafiya a yankin, baya ga lalubo hanyar warware rikicn Syria.

Turkiya dai ta sha korafi kan nauyin da aka jibga mata na kula da kimanin ‘yan gudun hijirar Syria miliyan hudu da ke rayuwa a kasarta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.