Isa ga babban shafi
Bankin Duniya

Bankin Duniya zai yaki talauci a kasashen da ake rikici

Bankin Duniya ya kaddamar da sabon yunkurin yaki da matsanancin talauci, inda zai fadada aikinsa a kasashen da ke fama da tashe-tashen hankula.

Kasar Syria na cikin jerin kasashen duniya da rikici ya jefa cikin mummunan hali
Kasar Syria na cikin jerin kasashen duniya da rikici ya jefa cikin mummunan hali OMAR HAJ KADOUR / AFP
Talla

Shirin bankin duniyar na tsawon shekaru biyar, zai magance abin da bankin ya kira bukatar gaggawa, yana mai gargadi kan yadda rikice-rikice ke haddasa talauci tare da wawushe asusun hukumomin agaji.

Sabon shirin zai mayar da hankali kan kasashen da ke fama da bakin talauci ko kuma matsakacin talauci da kuma kasashen da ke fuskantar matsalar kwararar ‘yan gudun hijira.

A wani mataki da ba a saba ganin irinsa ba, shirin bankin duniyar zai daure wajen ci gaba da samar da kayayyakin agaji koda kuwa ana kan ganiyar rikici a kasashen da za su ci gaciyar shirin.

Shugaban bankin duniyar, David Malpass ya ce, kasashen na bukatar samun ababan more rayuwa da suka hada da sufuri kafin kawo karshen matsanancin talauci har ma da rikice-rikice.

Bankin duniyar da aka kafa shi domin sake gina nahiyar Turai bayan yakin duniya na II, ya ware Dala biliyan 18.7 domin tallafa wa kasashen da rikci ya daidaita.

Sama da mutane miliyan 70 sun rasa mahallansu a sanadiyar rikice-rikice a kasashen duniya, yayin da ake da ‘yan gudun hijira miliyan 26.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.