Isa ga babban shafi

Amurka na shirin zuba jari wasu kasashen Afirka

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, ya fara ziyar aiki Asabar din dan a wasu kasashen Afirka da suka hada da Senegal da Angola da Habasha, wadanda a cewarsa suka taka rawar gani a dimokradiyar kasashensu, duk da cewar nahiyar na fuskantar koma baya a fannin ‘yan shekarun nan.

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo
Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo Kevin Lamarque/Reuters
Talla

Ziyarar babban jami’in irinsa ta farko zuwa yankin kudu da saharar Afirka na zuwa ne, a dai-dai lokacin da Kasar Amurka ke shirin rage sojojinta daga Nahiyar tare da tsaurara ko hana Visa shiga kasar ga wasu kasashen zuwa Amurka.

Sai da rahotanni sun ce, Pompeo zai yi kokarin samar da kyakkyawar dangantaka, da hadin gwiwar tsakanin Amurka da kasashen na Afirka da kasar China ke kara samun tago mashi.

Jami’an Amurka sunce Pompeo zai karfafa dangantakar kasuwanci da zuba jari a nahiyar Afirka, da akayi kiyasin al ‘ummarta zata ninka daga shekarar 2050.

Sai dai ana ganin abune mai wuya duba da yadda kasar China ta yi nisa a harkokin kasuwanci da zuba jari a kasashen na Afirka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.