Isa ga babban shafi
China

Coronavirus ta yi mummunar barna a karshen mako

Adadin mutanen da cutar Coronavirus ta kashe ya zarce 900 a China, yayin da cutar ta lakume rayuka 97 a jiya kadai, adadin da ba a taba ganin irinsa a rana guda tun bayan barkewar cutar.

Wasu daga cikin masu dauke da cutar Coronavirus kwance a asibitin Wuhan na China
Wasu daga cikin masu dauke da cutar Coronavirus kwance a asibitin Wuhan na China China Daily via REUTERS
Talla

An samu akasarin sabbin mamatan ne a Hubei da ke lardin mahaifar wannan cuta, kuma kawo yanzu, adadin wadanda cutar ta kashe ya zarta 774 da cutar SARS ta lakume a shekarar 2002-2003.

Wannan an zuwa ne bayan Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta ce, an samu sassaucin cutar a cikin kwanaki hudu da suka gabata a Hubei, amma ta yi gargadin cewa, akwai yiwuwar tashin alkaluman mamatan.

Kimanin mutane dubu 37 da 200 na dauke da cutar ta Coronavirus a China wadda ta fara bayyana karshen shekarar bara a Wuhan, babban birnin Hubei, inda al’ummar yankin ke fafutukar neman abin masarufi.

Cutar ta tilasta wa gwamnatin China rufe daukacin birane a daidai lokacin da al’umma ke nuna bacin ranta kan zargin gwamnatin da yin sakacin tunkurar cutar musamman ma ganin yadda annunbar ta kashe likitan da ya fara fallasa ta.

Kasashen da wannan cuta ta bazu a duniya sun hada da Amurka Jamus da Faransa da Rasha da Spain da Finland da Sweden da Belgium da Italiya.

Sai kuma Hadaddiyar Daular Larabawa da India da Malaysia da Taiwan da Australia da Vietnam da Korea ta Kudu da Thailand da Singapore da Canada da Cambodia da kuma Sri Lanka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.