Isa ga babban shafi
Amurka-Faransa

Amurka da Faransa na tattaunawar warware rikicin kasuwancinsu

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da takwaransa na Amurka Donald Trump sun amince kasashen biyu su ci gaba da tattauwa don warware sabanin da ke tsakaninsu tun bayan da Faransar ta lafta haraji kan manyan kamfanonin sadarwar Amurkan.

Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron. Ludovic Marin/Pool via REUTERS
Talla

Matakin wanda ke da nufin dakatar da yakin kasuwanci tsakanin kasashen biyu na zuwa ne bayan da Shugaba Macron na Faransa ya sanar da lafta haraji kan kanfanonin sadarwa Amurka da suka kunshi Google, Apple, Facebook, Amazon da kuma Netflix.

A jawabin ministan kudin Faransa Bruno Le Maire ga manema labarai gabanin ganawa da takwarorinsa ministociun kudin kasashen Turai, ya bayyana cewa kasashen biyu sun cimma matsayar ci gaba da tattaunawa don dakatar da rikicin kasuwancin da ya fara girmama tsakaninsu.

Wata majiyar Diflomasiyyar Faransa ta ce, shugaban na Faransa Emmanuel Macron da takwaransa na Amurka Donald Trump sun tattauna kan batun ta wayar tarho tun a shekaran jiya Lahadi, inda Amurkan ta sha alwashin dakatar da matakin sanya takunkumai kan hajojin Faransar, yayinda za su ci gaba da tattaunawa har zuwa karshen shekarar nan don magance matsalar.

Cikin sakon Twitter da Emmanuel Macron na Faransa ya wallafa a shafinsa na Twitter shugaban ya bayyana tattaunawarsa da Donald Trump a matsayin mai matukar muhimmanci da za ta bayar da kariya ga kasuwancin kasashen biyu, inda a bangare guda Donald Trump ya mayar da martani ta hanyar nuna alamun jinjinawa ga rubutun na Macron.

Haka zalika sanarwar da fadar White House ta fitar yau Talata, ta bayyana tattaunawar ta Trump da Macron a matsayin mai matukar muhimmanci da za ta magance rikicin da ke tsakaninsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.