Isa ga babban shafi
Turkiya-Libya

Erdogan ya gargadi Turai kan yiwuwar sake barkewar rikici a Libya

Shugaban Turkiya Recep Tayyib Erdogan ya gargadi kasashen Turai kan irin barazanar ta’addancin da ke tunkarosu matukar suka zuba ido Libya ta sake afkawa cikin yakin da zai tarwatsa kasar.

Shugaban Turkiya Recep Tayyib Erdogan.
Shugaban Turkiya Recep Tayyib Erdogan. Murat Cetinmuhurdar/Presidential Press Office/Handout/REUTERS
Talla

Cikin wata sanarwa da Turkiya ta fitar yau Asabar gabanin fara taron zaman lafiyar Libya a Berlin, Erdogan ya bayyana cewa matukar Turai ta gaza bayar da cikakken goyon baya wajen wanzuwar halastacciyar gwamnatin Libya, hakan na matsayin babban butulci ga dokokin kare hakkin dan adam da Demokradiyya.

Shugaba Erdogan wanda ke goyon bayan Firaminista Fayez Al-Sarraj, ya nanata cewa, kungiyoyin ta’addanci ciki har da ISIS da Alqa'eda wadanda aka kakkabe su a Syria na iya samun cikakkiyar damar kafa sansanonin ta’addanci matukar gwamnatin Libya ta fadi.

A bangare guda suma kasashen da ke makwabtaka da Libya suka bukaci, daukar matakai don kaucewa sake fuskantar bazuwar makaman da za su ci gaba da rura wutar hare-haren ta’addancin da suke fuskanta.

Cikin Sanarwar da kasashen Chadi, Sudan Algeria Tunisia da kuma Masar suka fitar sun bukaci daukar mataki wajen ganin rikici bai sake rincabewa a kasar ba, wanda suka bayyana da ummulaba’isin rashin tsaron da kasashensu ke fuskanta a yanzu haka.

Moussa Faki shugaban kungiyar Afrika, wanda tuni ya isa Berlin don shiga tattaunawar zaman lafiyar libya, ya bayyana cewa, zaman lafiyar Libya shi ne zaman lafiyar nahiyar Afrika.

Ko a baya-bayan nan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da ya jima yana zargin Libya da assasa yaduwar makamai a kasashen Afrika, ya ja hankali kan kalubalen da kasashen Afrikan ka iya fuskanta matukar yaki ya sake barkewa a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.