Isa ga babban shafi
Brazil

Lula ya samu tarbe daga magoya bayan sa

Tsohon Shugaban kasar Brazil Lula Da Silva ya samu gaggarumin tarbe daga magoya bayan sa ,yan lokuta da fitowar sa daga gidan yari Curtiba da ake tsare da shi bayan hukuncin wata kotu da ke barazanar haifar da rarrabuwar kanu a fagen siyasar kasar.

Tsohon Shugaban Brazil Lula Da Silva da magoya bayan sa
Tsohon Shugaban Brazil Lula Da Silva da magoya bayan sa REUTERS/Rodolfo Buhrer
Talla

Lula da ya share kwanaki 580 a tsare na cikin dubban yan kurkuku da aka bari su yi tafiyarsu, bayan kotun kolin kasar ta yi watsi da karar da hukumomin kasar suka shigar, na neman ci gaba da tsare masu laifin da aka yanke wa hukunci bayan sun yi rashin nasara a daukaka karar da suka yi.

Bangaren Shugaban kasar mai ci Jair Bolsonaro bai nuna damuwa ba dangane da sallamar tsohon Shugaban kasar daga gidan yari,yayinda wasu ke danganta Bolsonaro a matsayin babban dan adawa ga tsohon Shugaban Lula Da Silva.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.