Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya dada shiga tsaka mai wuya a Amurka

Ana zargin shugaban Amurka Donald Trump da neman taimakon Firaministan Australia Scott Morrison wajen kawo cikas ga binciken Robert Mueller kan zargin da ake yi wa Rasha na yin katsalandan a zaben Amurka na 2016.

Shugaba Donald Trump na Amurka
Shugaba Donald Trump na Amurka REUTERS/Leah Millis
Talla

Jaridar New York Times ce ta bankado wannan zargi, inda ta ce Firaministan na Australia ya yi tafiye-tafiye zuwa kasashen Italiya da kuma Birtaniya don tara bayanai kan Mueller bisa umurnin Trump.

Wannan sabon zargi na zuwa ne yayin da Majalisar Wakilan Amurka ta kaddamar da shirin tsige shugaban bisa zargin yin matsin lamba ga takwaransa na Ukraine don sa ido kan tsohon mataimakin shugaban kasar da ke zama daya daga cikin manyan masu adawa da shi a siyasance wato, Joe Biden.

A cikin watan Afrilun da ya gabata ne aka fitar da sakamakon binciken Mueller wanda bai nuna karara cewa, Mr. Trump ya aikata babban laifi ta hanyar hada baki da Rasha ba a zaben na 2019.

Kodayake, binciken na Mueller bai wanke Trump kacokan ba, abin da ya sa shugaban ya caccaki binciken tare da bayyana shi a matsayin bita da kullin siyasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.