Isa ga babban shafi
Duniya

Musayar fursunoni tsakanin Rasha da Ukraine

A karon farko Rasha da Ukraine sun yi musayar fursononi a yau asabar, matakin da akasarin kasashen Duniya suka yaba da shi.

Oleg Sentsov, daya daga cikin mutanen da Rasha ta sako zuwa Ukraine
Oleg Sentsov, daya daga cikin mutanen da Rasha ta sako zuwa Ukraine REUTERS/Gleb Garanich
Talla

Fursinonin da Rasha ta mayar da su zuwa Ukrain sun hada da sojan ruwan nan 24 da Rasha ta kama da jirgin ruwan dake dauke da su a yankin Crimea, banda haka Rasha ta mika mai shirya Fina-Finan Oleg Sentsov wanda da jimawa kasashen Duniya suka bukaci Rasha ta sallame shi.

Waziyar Jamus Angela Merkel da Shugaban Faransa sun yaba matuka da halin da kasashen biyu suka cima da kuma ta kai su ga musayar fursinoni, biyo bayan yakin da kasashen biyu suka fada a gabacin Ukrain tun a shekara ta 2014 da kuma ya hadasa mutuwar kusan mutane 13.000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.