Isa ga babban shafi
Tarayyar Turai

EU za ta dauki mataki kan Amurka

Kungiyar Turai ta ce za ta dauki matakan da suka wajaba ciki har da yin amfani da dokokin Hukumar Kasuwanci ta Duniya WTO, domin kin mutunta sabbin takunkuman kasuwanci da Amurka ta kakaba wa Cuba.

Jami'ar Diflomasiyar Kungiyar Tarayyar Turai, Federica Mogherini
Jami'ar Diflomasiyar Kungiyar Tarayyar Turai, Federica Mogherini REUTERS/Francois Lenoir
Talla

Shugabar Ofishin Kare Manufofin Ketare a Kungiyar Turai Federica Moghreni, ta ce dokar ta Amurka da ake kira Helms-Burton Act wadda ta fara aiki a jiya Alhamis, ko shakka babu za ta shafi harkokin kasuwanci tsakanin Turai da Cuba.

Karkashin wannan doka, gwamnatin Amurka na da hurumin shigar da kara a gaban kotun kasar, domin kwace kadarorin kasashen da ke huldar cinikayya da Cuba.

Kusan dukannin manyan kasashen Turai da suka hada da Faransa, Jamus, Spain da kuma Italiya, na da hannayen jari a cikin kamfanonin kasar ta Cuba, kuma karkashin dokar Amurka za ta iya kwace masu kadarorinsu.

Ita ma kasar Canada, wadda ta zuba makuden kudade a matsayin hannayen jari a Cuba, wannan sabuwar doka ta shafe ta, to sai dai Moghereni, ta ce matakin ya yi hannun riga da dokokin kasa da kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.