Isa ga babban shafi
EU-Amurka

EU za ta lafta wa Amurka harajin Dala biliyan 12

Kungiyar Tarayyar Turai na shirin lafta wa Amurka harajin da ya kai Dala biliyan 12 a matsayin martani kan matakin da gwamnatin kasar ta dauka na bayar da tallafi ga kamfanin jiragen sama na Boeing, abinda ya saba wa dokokin Cibiyar Kasuwanci ta Duniya.

EU ta dauki matakin lafta wa Amurka haraji a matsayin martanin bai wa kamfanin Boeing tallafi da kuma barazanar da Amurka ta yi na sanya wa EU harajin Dala 11
EU ta dauki matakin lafta wa Amurka haraji a matsayin martanin bai wa kamfanin Boeing tallafi da kuma barazanar da Amurka ta yi na sanya wa EU harajin Dala 11 Simon Dawson/Bloomberg via Getty Images
Talla

Daga cikin kayayyakin Amurka da Kungiyar Tarayyar Turai ta ce, za ta lafta wa harajin har da ruwan zuma da safayen motoci da Amurkan ke shigar da su nahiyar Turai, matakin da ka iya farfado da yakin kasuwanci tsakanin bangarorin biyu.

Kwamishiniyar Kasuwancin Tarayyar Turai, Cecilia Malmstrom ta ce, dole ne kamfanonin kasashen Turai a dama da su a fagen gogayyar kasuwanci cikin adalci, tana mai cewa, wajibi ne su kare masana’antunsu.

Harajin na Dala biliyan 12 da EU ke fatan lafta wa Amurka na zuwa ne bayan ita ma Amurka ta yi barazanar lafta wa Turai harajin Dala biliyan 11 saboda tallafin da ita ma ta bai wa kamfanin jiragen sama na Airbus.

Sai dai Cibiyar Kasuwanci ta Duniya ce za ta kayyade adadin harajin da kowanne bangare zai lafata wa dan uwansa, kuma ana ganin ko kadan harajin ba zai kai yawan kudin da bangarorin biyu ke ambata ba.

Kimanin shekaru 14 kenan da kamfanonin Boeing da Airbus suka gamu da rikicn kasuwanci, in da Amurka da Tarayyar Turai ke zargin juna da tallafa wa jiragen da kudin gwamnati da zummar kere takwarorinsa a fagen gogayyar kasuwanci, matakin da ya saba wa dokokin Cibiyar Kasuwanci ta Duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.