Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka ta kulla yarjejeniyar makamai ta Dala biliyan 1

Sakamakon wani bincike da aka gudanar, ya nuna cewa Amurka ta kulla yarjejeniyar cinikin makamai masu linzami na sama da dala biliyan 1 cikin watanni uku kacal, bayan ficewa daga yarjejeniyar haramta kera makaman masu linzami da kasashen duniya suka cimma.

Nau'in makami mai linzami
Nau'in makami mai linzami (@wikipedia.org)
Talla

Beatrice Fihn, shugaban wata kungiya mai fafutukar yaki da kera muggan makamai ta kasa da kasa da ta lashe kyautar zaman Lafiya ta Nobel kan kokarinta, ta yi gagadin cewa janyewar da Amurka ta yi daga cikin yarjejeniyar kera makaman, tamkar tsokano barkewar sabon yakin cacar baka ne.

A watan Oktoban shekarar bara shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana janyewa daga cikin yarjejeniyar INF da ta haramta manyan makamai masu linzami da ke cin matsakaicin zango da Amurka ta kulla da Tarayyar Soviet, wato Rasha a cikin shekarar 1987.

Trump ya zargi Rasha da saba ka’idojin yarjejeniyar ta hanyar kera wasu sabbin makamai masu linzami da ke cikin ajin wadanda yarjejeniyar ta INF ta haramta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.