Isa ga babban shafi

"Manyan kasashe basa daukar mataki kan take hakkin Bil Adam"

Kungiyar kare Hakkin Bil Adama ta Human Rights Watch, ta zargi manyan kasashen duniya da kauda idanun su kan yadda ake take hakkin Bil Adama sakamakon matsalolin cikin gidan da suka addabe su.

Daraktan Kungiyar kare Hakkin Bil Adama ta Human Rights Kenneth Roth. 16/01/2019.
Daraktan Kungiyar kare Hakkin Bil Adama ta Human Rights Kenneth Roth. 16/01/2019. REUTERS/Hannibal Hanschke
Talla

Kungiyar ta sanar da haka ne yayin gabatar da rahotan ta na wannan shekara.

Rahotan kungiyar na bana yace kasar Amurka da manyan kasashen Turai da suka mayar da hakkin Bil Adama a matsayin daya daga cikin manufofin su a kasashen waje tun lokacin yakin cacar baka, a yau sun kauda hankali daga kai.

Daraktan kungiyar Kenneth Roth, yace matakin kalubalantar take hakkin Bil Adama na raguwa, inda yake komawa kan kungiyoyin cikin gida.

Roth yace shugaba Donald Trump na Amurka ya mayar da hankali wajen rungumar shugabannin dake kama karya, rikicin ficewa daga kungiyar kasashen Turai ya mamaye Birtaniya, yayin da shugaban Faransa Emmanuel Macron ke kalamai masu dadi amma kuma baya iya aiwatar da su.

Daraktan yace ita ma Angela Merkel wadda tayi ficde wajen yaki da matsalar, yaki da masu tsatsauran ra’ayin cikin gida ya dauke mata hankali.

Rahotan ya yabawa kasashe 57 dake kungiyar kasashen Musulmi ta IOC da suka tashi tsaye domin kalubalantar yadda ake cin zarafin yan kabilar Rohingya a Myanmar, duk da yake kasashen basu ce komai ba kan yadda China ke cin zarafin Musulmi 'yan kabilar Uighur.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.