Isa ga babban shafi
Amurka-Saudiya

Shugaba Trump ya bukaci samun karin haske dangane da kisan Khashoggi

Bayan da hukumar Leken asiri dake Amurka CIA ta zargi Yariman Saudiya da kashe Kashoggi tareda mika rahoton binciken zuwa Shugaba Donald Trump,Shugaban ya bayyana cewa nan da kwana biyu za a gano gaskiyar lamarin.

Jamal Khashoggi
Jamal Khashoggi AFP 2018 OZAN KOSE
Talla

A jiya asabar ne mataimakin Shugaban Amurka Mike Pence ya sheida cewa hukumomin Amurka za su bayar da hadin kai don gani an zakulo mutanen dake da hannun a kisan dan jaridar nan Jamal Khashoggi , Hukumar Cia ta mika rahoton binciken zuwa Shugaban kasar Donald Trump ,wanda ya kuma tabbatar da cewa nan da kwana biyu nan gaskiya za ta bayyana dangane da kisan dan jaridan .

An gudanar da sallar jana’izza ga dan jarida Jamal Khashoggi a birnin Santambul na Turkiya ranar juma’a inda dubban mabiya addinin Islama suka kasance a garin.

An gudanar da sallar a masallacin Fatih da ke tsakiyar birnin Santambul na Turkiyya, ciki har da Iyalansa, 'Yan uwa da kuma sauran magoya baya dama daidaikun musulmi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.