Isa ga babban shafi
Myanmar

Majalisar dinkin duniya ta ce komawar yan Rohingya gida ya yi sauri.

Babbar Mai bincike na MDD dake binciken zargin cin zarafin ‘yan kabilar Rohingya na kasar Myanmar Uwargida Yanghee Lee ta roki mahuntan kasar Bangladesh da su wa Allah su jingine shirinsu na mayar da ‘yan Rohingyan dake gudun hijira gida domin har yanzu akwai matsala.

wasu yan gudun hijirar kabilar Rohingya a kasar Myamar
wasu yan gudun hijirar kabilar Rohingya a kasar Myamar RFI/Sarah Bakaloglou
Talla

Sama da ‘yan Rohingya dubu 700 yanzu haka ke samun mafaka a Bangladesh bayan da suka gujewa cin zarafin da jam’ian tsaron kasar Myanmar ke yi masu.

Myanmar da Bangladesh sun amince zuwa 30 ga watan daya gabata za’a mayar da masu gudun hijiran, amma kuma mai binciken ta MDD na ganin an yi gaggawa.

A ranar larabar da ta gabata ne ne 31 ga watan Octoban da ya gabata wani babban jami’an gwamnatin Bama ya tabbatar da sake komawar kimanin yan kabilar Rohingya dubu 2000 gida daga sansanin yan gudun hijira dake kasar Bangladesh.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.